Sakamakon binciken da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta yi ya nuna cewa mutane sun fi son yin amfani da maganin gargajiya maimakon maganin asibiti.
NAN ta gudanar da wannan bincike a jihohin Filato, Taraba, Benuwai da Nasarawa.
Bisa ga sakamakon binciken da aka gabatar dalilan da ya sa mutame ke amfani da maganin gargajiya sun hada da rashin ingancin warkar da cututtuka da maganin bature ke da shi, yawan bata lokaci a asibiti, tsadar magani da kuma camfe-camfe na mutane.
Jihar Benuwai
Wasu mazauna jihar Benuwai da suka dade suna amfani da maganin gargajiya sun ce suna amfani da sauyoyi da ganyayyakin itattuwa dabam-dabam da suka hada da ganyen gwaiba, lemu, ayaba, dogon yaro (neen) zogale, da dai sauran su wajen warkar da cututtuka da dama da wadandan maganin bature ba ya yi musu.
Cututtuka da suka hada da ciwon sanyin kashi (Arthritis), yawan zafi a jiki, zazzabin cizon sauro, ciwon typhoid, basir da sauran su.
Boniface Kper dake zama a Makurdi ya ce a fannin gyaran kashi masu gyaran kashi na gargajiya ne mutane suka fi na’am dasu idan aka samu karaya maimakon na asibiti.
Jihar Filato
Wadandan ke amfani da maganin gargajiya a jihar Filato sun ce maganin gargajiya ya fi inganci musamman wajen warkar da cututtukan da suka hada zazzabin cizon, typhoid, amai da gudawa, da sauran su.
Wani ɗan jarida mai suna, Aminu Kogi ya ce ya yi shekaru sama da 20 yana amfani da maganin gargajiya domin ma shi gadon sa yayi wajen iyayen sa. Ya ce shi yakan hada kuma yasha.
“Sassaken itacen kwakwa idan ka dafa ka sha ruwan yana maganin tari sannan wasu ganyayyakin idan ka kona su ka busar ka nika shi ya zama gari aka sha yana maganin tari.
A Lafia, Jihar Nasarawa, wata mata mai suna Titi Joseph ta ce arha, saukin samu da ingancin maganin gargajiya na daga cikin dalilan da ya sa take amfani da shi.
Titi ta ce tana yawan amfani da magani gargajiya da ake kira agbo.
“Cikin Kofi daya Naira 50 ake saida shi, idan ka kwankwada zai warkar da kai daga cututtuka kamar zazzabin cizon sauro, typhoid, ciwon siga da sauran su.