Korona na cigaba da yaduwa a nahiyar Afrika sai dai yaduwar cutar bai kai kamar yadda ta ke yaduwa ba a kasar Amurka.
Sakamakon wani bincike ya nuna cewa hakan na da nasaba ne da karfin garkuwan jikin da mutanen Afrika ke da shi sabo da sabawa da jikin su yayi da yaki da cututtuka dabam dabam.
Zuwa yanzu alkaluma daga ‘Worldometers’ sun nuna cewa sama da mutum miliyan biyu sun kamu da korona a Nahiyar Afrika.
Mutum sama da miliyan 1.7 sun warke sannan mutum 48,000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
Ofishin WHO dake Brazzaville kasar Kongo ya sanar da haka.
Kasashen Afirka ta Kudu, Algeria da Kenya ne kasashe a Nahiyar da suka fi kamuwa da cutar.
Kasar Afrika ta Kudu mutum 757,144 sun kamu, 20,556 sun mutu.
A Algeria mutum 70,629 sun kamu, 2,206 sun mutu.
Kasar Kenya ta samu mutum 72,686 da suka kamu da mutum 1,313 da Suka mutu
Kasar Amurka
Zuwa yanzu alkaluma suka nuna cewa sama da mutun 250,000 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar a Amurka.
‘Wordometer’ da ke fidda alkaluman bayanan halin da kasashen duniya ke ciki game da annobar ya fitar cewa ana cigaba da samun hau-hawan yawan mutanen dake kamuwa da cutar a kasar Amurka da kuma wadanda ke rasuwa a kullum.
A makon da ya gabata akalla mutum 1,167 suka mutu a cikin uni daya.
A yanzu dai Amurka ita ce kan gaba wajen samun yawan mutanen da korona ta kashe a duniya.
Mutum miliyan 11.8 me suka kamu da cutar Amurka a yanzu haka.
A yanzu mutum miliyan 56 ne suka kamu da cutar sannan miliyan 1.3 sun mutu a duniya