Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa rashin cika alkawarin da ‘yan siyasa ke dauka a lokacin kamfen, shi ne babban dalilin da ya sa dimbin jama’a ba su fitowa jefa kuri’a a ranakun zabe.
Yakubu ya ce ƴan Najeriya sun gaji a kullum shekara da shekaru ana yi masu alkawari iri daya, amma duk wanda ya dauki alkawarin, idan an zabe shi ba cikawa ya ke yi ba.
Ya yi wannan bayani ne a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai lura da harkokin zabe, a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin domin kara tantance shi a karo na biyu.
A lokacin tantancewar, an tambayi shugaban na INEC dalilin da ya sa ba a ganin mutane makil na jefa kuri’a.
Cikin dalilan da ya kawo, sun hada da rashin cika alkawurran da ‘yan siyasa ke daukar wa jama’a a lokacin kamfen, tashe-tashen hankula, hargitsi da jagaliyanci da kuma rashin wadataccen lokutan wayar wa jama’a kai.
“Gaskiyar magana jama’a na tsoron fita wurin jefa kuri’a saboda rikicin da ake yi a ranar zabe. Kowa ba tsoron kada hargitsi ya ritsa da shi. Shi ya sa jama’a su ka gwammace su zauna a gida, su zama ‘yan kallo.
“Wasu lokuta kuma mutane kan tuna wadanda su ka zaba a shekaru hudu da su ka gabata sun yi masu alkawurran da ba su cika ba. To sai su yi tunanin don me kuma za su sake bata lokacin su da saida ran su su koma sake zaben wadanda ba dai cika masu wani sabon alkawarin za su yi ba?”
Yakubu ya ce abu na uku shi ne kara wayar wa jama’a kai da muhimmancin su je su jefa kuri’a. Wannan kuwa a cewar sa, ayyukan jam’iyyun siyasa ne da kuma Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA).
PREMIUM TIMES ta gano cewa tun daga zaben 2003 har zuwa na 2015, a kowane zabe yawan masu jefa kuri’a raguwa ya ke yi.
Na 2019 ne mafi karancin masu jefa kuri’a da kashi 34.7 kacal na adadin yawan wadanda su ka yi rajista.