Gwamna Rotimi Akeledolu na Jihar Ondo, ya bayyana cewa bai ga wani abin damuwa ba don bankin CBN ya garkame asusun ajiyar wadanda su ka shirya zanga-zangar #EndSARS.
Akeredolu ya yi wannan bayani a lokacin da aka yi hira da shi, ranar Laraba da Gidan Talbijin na Channels.
CBN ya garzaya kotu ya kai kuka cewa a ba shi iznin kulle asusun na mutum 19 da kuma na wani kamfani daya mai suna Gratefield Nigeria Limited.
Wannan kamfani shi ne ya dauki nauyin abincin da aka rika ci a wurin zanga-zanga kuma ya biya kudade ko ya dauki nauyin watsa zanga-zangar a kafafen yada labarai.
Kotu ta aika da sammacin sanarwa da umarnin gaggauta kulle asususu 20 ga bankunan da su ka hada da Access Bank, Fedility, First Bank, UBA da kuma Zenith, bisa umarnin CBN na a rufe asusun.
Akeredolu ya ce shi ya na ganin CBN ta cika aikin da ya kamace ta ne ta yi. Don haka, ta yi daidai.
“Idan ka san ka na da gaskiya, ai don an kulle asusun ka ba laifi ba ne. Kawai kotu za ka je ka bada bayanin shaidar ba wata harkalla ka ke yi da asusun ba. Shikenan sai a bude maka abin ka.
“Ni din nan an taba kulle nawa asusun. Na je kotu na yi bayani. Kuma an sha kulle na ƴan siyasa da dama.”
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin kulle asusun bankunan da kuma sunayen wadanda aka kulle asusun na su, su 20.
Ta kuma buga labarin yadda ƴan sanda su ka fara yi wa wasun su tsintar-farin-balbela, bayan wasun su sun fito suna shelar fara wata sabuwar zanga-zanga.
Tuni dai an gurfanar sa wasu da dama a kotu, har an fara shari’a.
Sai dai kuma mutane da dama na ganin bai kamata a rika kama su ba, gudun kada wani tunzurin ya sake tashi mai kama da wanda aka yi a baya.
Ita dai Fadar Shugaban Kasa ta jaddada cewa dukkan masu hannu a zanga-zangar, sai sun yaba wa aya zakin ta.