Cututtukan da basu jin maganin na gab da zama annoban da za a yi fama da su nan gaba a duniya – FAO

0

Hukumar kula da ingancin abinci ta majalisar dinkin duniya FAO tace idan ba a gaggauta daukan matakai ba cututtukan da basu jin magani za su zama annoban da za a yi fama da su nan gaba a kasashen duniya.

Hukumar ta fadi haka ne a shafin ta na yanar gizo ranar Laraba.

Cututtukan da basu jin maganin cututtuka ne dake da wahalar warkewa koda an sha maganin dake warkar da su musamman cututtukan da kwayoyin cutar ‘Bacteria’ ke haddasa su.

Magani ‘Antibiotics’ ne ke warkar da kwayoyin cutar ‘bacteria’ sannan maganin kan daina aikin kawar da kwayoyin cututtukan ne idan ana amfani da shi ta hanyoyin da bai kamata ba.

A dalilin haka FAO ta yi kira ga manoma da masu dafa abinci, masu sarrafa abinci da masu amfani da shi da su hada hannu wajen ganin an kawar da wannan matsala.

Hukumar ta ce rashin yin haka zai gurgunta fannin kiwon lafiya, noma da tattalin arzikin kasashen duniya.

Bincike ya nuna cewa akalla mutum 700,000 ne ke mutuwa duk shekara a dalilin cututtukan da basu jin magani.

Sannan adadin yawan cututtukan da basu jin magani na karuwa ne a kullum.

Shugaban hukumar FAO Maria Semedo ta yi kira ga kowani fanni da su fito a hada hannu wajen kawar da cututtukan da basu jin magani domin gujewa barkewar wata sabuwar annobar a duniya.

A ranan 16 ga watan Nuwanba ne PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda masana kimiya da likitoci suka koka kan yadda mutane ke amfani da maganin Antibiotics da yawa ba tare da umarnin likita ba wanda hakan ya sa magungunan suka daina aiki a jikin mutane.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce sakamakon haka ya sa ake samun cututtukan da basu jin magani, karancin maganin Antibiotics sannan wanda ke da karfin yin aiki a jikin mara lafiya na da dan karan tsada.

Kungiyar ta yi kira ga mutane da su daina shan magani batare da likita ya basu umarnin yin haka ba.

Share.

game da Author