CIWON NIMONIYA: Ƙungiya ta raba wa mata 1,650 radiyo domin sauraren labarai a jihar Jigawa

0

Kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Save the Children’ ta raba wa mata 1,650 radiyo a karamar hukumar Kiyawa dake jihar Jigawa.

Jami’in kungiyar Abdullahi Magama ya ce dalilin raba wa mata wadannan radiyo shine don su rika sauraren shirye-shiryen da ake yi na kiwon lafiya domin amfanin kan su da ƴaƴan su.

Sannan kuma a duk lokacin da ake wani shiri na kiwon lafiya mata za su iya buga waya kaitsaye kyauta domin a wayar musu da kai a filin shirin.

Bayan haka dagacen Kiyawa, Adamu Aliyu wanda ya yi tsokaci a madadin sarakunan jihar yayi Kira ga gwamnati da ta kara ware kudade domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Aliyu ya ce rashin yin haka na sa ana samun mace-macen marasa lafiya da sauran su.

Wasu daga cikin matan da aka raba wa radiyon kamar su Jamila Isma’il da Husseina Ismail sun yi murna matuka, sun ce wannan kokari da aka yi zai taimaka musu wajen samun karin bayani game da kiwon lafiyar su.

Sun ce ciwon Nimoniya cuta ce dake kisan yara musamman ‘ya’yan talakawa dake karkara.

Cutar Nimoniya

Ciwon sanyi na nimoniya cuta ce na sanyi dake kama hakarkarin mutum a dalilin shakan gurbataccen iska da kuma yawan amfani da abubuwa masu sanyi.

Cutar na daya daga cikin cututtuka biyar dake kisan yara kanana ‘yan kasa da shekara biyar a duniya.

Sakamakon binciken da jami’ar ‘John Hopkins’ ta yi ya nuna cewa nan da shekaru 10 masu zuwa Najeriya za ta iya rasa yara ‘ƴan kasa da shekaru biyar akalla miliyan biyu a dalilin kamuwa da cutar sanyi ‘Nimoniya’.

Share.

game da Author