Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kaddamar da wani sabon shiri na raba wa manoma bashin naira bilyan 2 da za su yi aniyar bunƙasa abinci, samar da aikin yi a fannin noma da kuma fadada fannonin tattalin arziki.
Shirin mai suna P-AADS, daraktan bunkasa hada-hadar kudade na CBN, Yusuf Philip ne ya sanar da shi a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar cikin watan Nuwamba da ake ciki.
Ya ce matasa akalla 370,000 za su samu aikin yi karkashin shirin na bunkasa aikin noma, mai suna Himma Dai Manoma (Accelerated Agriculture Development Scheme, AADS).
Shirin kamar yadda sanarwar da darakta Philip ya sa wa hannu, ta hadin-guiwa ce da gwamnonin jihohin kasar nan baki daya.
Sai dai kuma sanarwar ta ce za a aiwatar da shirin na AADS a karkashin tsarin P-AADS domin shigar da masu jari a cikin shirin, ta yadda za a gaggauta sassabe da share filaye da gonakin da za a yi wannan katafaren aikin bunkasa noma a kasar nan.
Ka’idojin da aka shimfida ga wadanda za su ci moriyar shirin bada naira bilyan biyu, kudaden da wadanda aka bai wa lamunin za su biya da amfanin gona da kuma gumin da su ka sha karcat wajen aikin sassabe da sharar filaye.
Akwai kuma kudin ruwa kashi 5 bisa 100 a duk shekara, wadanda za a fara tada lissafi tun daga 28 Ga Fabrairu, 2021.
Shirin Bada Ramce Ga Kananan Manoma, wato Anchor Borrowers’ Progmme (ABP) ne zai samar da kudaden akwatar da wannan shiri na AADS.
Cikin Nuwamba 2015 ne Buhari ya kaddamar da shirin Bayar Da Lamuni Ga Kananan Manoma (ABP), domin samar sa kayan noma da kudade ga kananan manoma (SHFs), ta yadda za su bunkasa noma har a cike gibin daina dogaro da abinci daga waje.
Manoman da ke cin moriyar wannan shiri sun hada manoman shinkafa, masara, alkama, auduga, rogo, doya, rake, tumatir da dangogin sa da kuma kiwon dabbobi.
Ana tura kudaden lamunin ne ga kananan bankuna wadanda a hannun su kananan manoma ke karbar basussukan, kuma a can ake biyan basussukan
Discussion about this post