Buhari Ga Matasan Najeriya: Ba na goyon bayan nuna karfin jami’an tsaro kan masu zanga-zangar lumana

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba ya goyon bayan nuna karfin jami’an tsaro a kan masu zanga-zangar lumana.

Buhari ya yi wannan bayani ranar Lahadi, makonni biyu bayan ya yi gum daga yin tir da wutar da sojoji su ka bude wa masu zanga-zangar #EndSAR a Lekki.

A wannan karon ma Buhari bai fito gadan-gadan ya yi tir da bude wutar da aka yi a Lekki ba.

A lokacin zanga-zangar lumana ta #EndSARS, jami’an tsaro sun yi amfani har da bindigogi su ka tarwatsa masu zanga-zangar lumana ca Lagos, Abuja, Oyo da Delta.

Bayanin Buhari na cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi.

Jawabi ne a matsayin sabon sa ga matasa a ranar Matasa ta Duniya, wato 1 Ga Nuwamba na kowace shekara.

Shehu ya ce Buhari bai samu damar halarta ba, amma Ministan FCT Abuja, Muhammad Bello ya wakilce shi.

“Kada a sake a ci zalin ko a ci zarafin wani da ya kiyaye bin doka da oda. Ko a layin shiga tasi ko a jerin zanga-zangar lumana.

“Saboda na yi amanna da ƴancin da doka ta bai wa kowa na gaggauta rusa jami’an SARS, tare da amincewa a yi tsarin ƴan sanda garambawul din da zai sa jama’a su inganta mu’amala tsakanin su.

“Kyale jama’a su yi zanga-zanga ba tsoro ko ragwanci ba ne, alama ce ta nuna amincewa da yin imani da dimokradiyya.”

Share.

game da Author