Boko Haram: Yadda manyan kasashen duniya ke tadiye kafafun Najeriya – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya ce kiri-kiri kuma da gangan manyan kasashen duniya ke kin sayar wa Najeriya manyan makaman da za ta yi amfani da su ta murkushe Boko Haram.

Lai ya yi wannan jawabi a ranar Litinin lokacin da ya kai ziyara ga Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai a Makurdi, babban birnin jihar.

Ministan ya ce abin akwai takaici da bacin rai ganin yadda manyan kasashen duniya ke ta yin tamaula da Najeriya wajen kin sayar mata da manyan makamai, a duk kasar da ta kai kokon barar ta.

Sai da kuma Minista Lai ya noke, bai ambaci kasa ko daya ballantana a ji ko a san aunayen su.

Amma kuma duk da rashin hadin kan da ya ce manyan kasashen ba su bai wa Najeriya, Lai ya ce kasar nan za ta yi bakin kokarin ta domin ta ga ta kakkabe Boko Haram kakaf baki daya.

“Ba za mu yi kasa a guiwa wajen kokarin kawar da Boko Haram ba. Amma kuma ya kamata a sani cewa ‘yan ta’addar nan fa daga kasashen waje ake daukar nauyin su da nauyin makaman su. Saboda haka Najeriya ita ma ta na bukatar hadin kai daga manyan kasashen duniya.

“Misali, mun yi ta kai gwauro mu na kai mari domin samo kandagarkin lakanin magance Boko Haram kwata-kwata. Amma duk inda mu ka je neman fahamin, ba su ba mu.”

Lai ya yi Allah-wadai da mummunan kisan yankan-ragon da Boko Haram su ka yi wa manoman shinkafa a jihar Barno a ranar Asabar har su 43.

Lai wanda ya ce ya je Makurdi ne domin bude ofishin Cibiyar Bunkasa Yawon Bude Ido, ya ce gwamnatin Buhari ta yi kokari matuka wajen fannin tsaro, kuma za ta ci gaba da yin kokarin har ta kawar da ta’addanci baki daya a kasar nan.

Share.

game da Author