BOKO HARAM: Najeriya za ta karbi jiragen yaki samfurin Super Tucano 6 daga Amurka – Hafsan Sojojin Sama

0

A wani gagarimin shirin yakin a-yi-ta-ta kare da Najeriya ke kan Boko Haram, Babban Hafsan Jiragen Sama, Sadique Abubakar kwanan nan za a aiko wa Najeriya wasu gingima-gingiman jiragen yaki guda shida.

Jiragen Samfurin Tashi-gari-barde (Super Tucano), su na daga cikin jiragen yaki 12 da Najeriya ta cake kudi ta yi oda a kera mata a Amurka, domin amfani da su wajen yi wa Boko Haram kwaf-daya.

Abubakar ya bayyana kusantowar kawo jiragen a lokacin da ya ke kare Kasafin 2021 na Hukumar Sojojin Sama a gaban Kwamitin Sojojin Sama.

Kuma Sojojin Sama din na jiran tsammanin kawo wasu kananan jiragen 19 duk domin yaki da Boko Haram.

An kuma tabbatar tuni an tura wasu zakakuran sojan sama daga nan Najeriya zuwa Amurka, domin samun horon yadda ake tuka wadannan manya-manyan jiragen yaki.

Da ya ke magana kan hare-haren da Sojojin Sama ke kai wa kuwa, Abubakar ya shaida wa kwamitin cewa an kai hare-hare na tsawon sa’o’i 60,000, wadanda rabin duk Arewa maso Yamma aka kai wa Boko Haram.

“Mu na sa ran jiragen yaki samfurin J-17 guda 3 daga Pakistan, Super Tucano 12 daga Amurka, sai M-171 guda 1. Daga cikin 12 din da za a kawo daga Amurka, kusan 6 ma sun kusa karasowa. Domin har ma mun tura wadanda za su tuka su da wadanda za su rika yaki a cikin su su na samun horo a Amurka.” Inji shi.

“Akwai zarata har 200 da yanzu haka ke karbar horo a kasashe 9 cikin duniya, domin sarrafa jiragen wadanda za a kawo a yaki ta’addanci a Arewa maso Gabas.”

Idan ba a manta ba, Buhari ya kamfaci kudade har dala milyan 469.4 ya aika Amurka matsayin kudaden jiragen da za a sayi jiragen yaki 12, ba tare da shawara ko neman amincewar Majalisar Dattawa ba.

Share.

game da Author