Shugabar Hukumar Harkokin ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana cewa hukumar na da masaniyar hukuncin daurin rai-da-rai da aka yi wa wasu ‘yan Najeriya da aka kama da laifin rika tura wa Boko Haram kudade.
An yanke masu hukuncin ne a Babbar Kotun Tarayya ta Abu Dhabi da ke karkashin Hadaddiyar Daular Larabawa bisa hannu da laifin rika tura wa ‘yan Boko Haram kudi.
“Mu na sane da hukuncin, amma ba za mu iya tabbatarwa ba tukunna.” Haka Kakakin Yada Labarai na Abike Dabiri-Erewa, mai suna Abdulrahman Balogun ya bayyana wa PREMIUM TIMES a ranar Litinin.
Wadanda aka yanke wa hukuncin su shida, sun hada da Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf Adamu, wadanda su biyun aka daure rai-da-rai.
Sauran hudun sun hada da Ibrahim Ali Alhassan, AbdulRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf da Muhammad Ibrahim Isa, su kuma kowa daurin shekara goma a kurkuku. Haka dai rahoton ya tabbatar.
Wadanda aka yanke wa hukuncin, an same su da laifin ne a cikin 2019, inda aka gano su na da alakar tura wa Boko Haram kudade, kuma su ka dauki shekaru su na tura kudaden ba tare da an gane ba. Har sai da dubun su ta cika.
Hukuncin kotu ya nuna cewa tsakanin 2015 da 2016, sun tura wa Boko Haram dala 782,000. Sai dai kuma makusantan su, sun ce jula-jular kudaden da su ka yi din, halastacciya ce, domin su ba su san wadanda su ka tura wa kudin ‘yan Boko Haram za su aikawa ba.
PREMIUM TIMES ta tuntubi Ministan Shari’a Malami domin jin ko Najeriya na da masaniyar shari’ar, amma bai bada amsa ba.
Amma wata jarida ta buga cewa Abubakar Malami na da masaniyar shari’ar, har ma Najeriya ta nemi a turo mata kwafen shari’ar da hukuncin da aka yi masu, domin ta yi nazari.
Amma ya ce har yau dai ba a turo wa Najeriya kwafen hukuncin ba.
Idan ba a manta ba, cikin 2014 wani Bature dan kasar Australiya mai suna Stephen Davis, ya zargi tsohon gwamnan Barno Ali Sheriff da hannu wajen daukar nauyin Boko Haram.
Davies dai mutum ne mai shiga tsakani wajen karbo wadanda ‘yan Boko Haram ke arcewa da su ko su yi garkuwa da su.
Sheriff ya karyata shi, kuma daga nan Davies bai bayar da wata shaida ba.
Discussion about this post