Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yaƙi da cin hanci da rashawa a kasar nan, ba zai tsallake kan duk wanda aka bincika aka tabbatar da ya yi ba daidai ba.
Kan haka ne Buhari ya ce babu wani wanda ya isa ko ake shakkun hukuntawa a kasar nan, matsawar an same shi da danne dukiyar al’umma.
Ya yi wannan bayani ne as lokacin da ya ke karbar rahoton kwamitin Ayo Salami wanda ya binciki Ibrahim Magu kan zargin azurta kai da kuma laifin yi wa kudin da ya kwato a hannun barayin gwamnati, abin nan da ake kira sata-ta-saci-sata.
Buhari ya ce ran sa baci matuka da aka wayi gari ana zargin hukumomin da aka nada su dakile cin hanci su na harkalla da kudade da kadarorin da su ka kwato.
Ya ce an kafa kwamitin Ayo Salami bisa a bisa yadda dokar kafa kwamitin bincike ta 2004 ta shimfida.
Ya ce an dora wa kwamitin nauyin binciken dukkan abin sa ya faru a EFCC, daga 2014 zuwa 2029.
Daga nan Buhari ya ce gwamnatin sa za ta datse duk wani kogin da ke kwararar da ruwa zuwa cikin gonakin da ake shuka harkalla har munanan amfanin gonar su na yin munanan yabanya.
“Mun sani cewa har yanzu akwai bangarorin cin hanci da rashawa da har yanzu ba a kai ga dakile su ba. Za mu shiga duk cikin gonakin mu, mu nome duk wata ciyawa da karangiya su ka hana shukar mu yado.”
A nasa jawabin, Salami ya shaida wa Buhari cewa masu shaidu 113 su ka bayyana a gaban kwamitin su ka bada ba’asi da shaida.
“Kwamitin ya karbi koke-koken mutum 46 a kan Magu.”
Salami shawarci Buhari a rika nada wa EFCC shugaba daga wani bangaren tsaro daban ba daga ‘yan sanda ba.