Tsakanin watan Satumba zuwa Disamba na 2019, an sungumi zunzurutun naira bilyan 4.6 na Ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje aka rika gabza ana tutturawa asusun ajiyar banki na wasu daraktoci da ma’aikatan da ke ma’aikatun uku.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da haka a wani binciken kwakwaf da ta yi. Kuma ta mallaki takardun da su ka tabbatar da cewa tuttura kudaden duk harkalla ce.
PREMIUM TIMES ta tura wa Ma’aikatar Makamashi, wato hasken lantanki wasikar neman rekod din kidaden da aka tura. Amma sai aka amsa da cewa naira milyan 157 ne kadai aka tura a Asus use mutane 127.
Sai dai kuma kwafe-kwafen takardun bayanan sa ke hannun PREMIUM TIMES, ya tabbatar ce karya ma’aikatar ke yi.
A yanzu dai Ma’aikatar Makamashi ita kadai ta ke, an cire ta karkashin rukunin ma’aikatun da ke karkashin Minista Raji Fashola, aka nada mata Minista Sale Mamman.
Amma dai a lokacin da aka gabji makudan kudaden aka yi watanda da su, ma’aikatar makamashi wato lantarki, a hannun Fashola ta ke.
Yadda Mutum 21 Su Ka Jide Naira Bilyan 4.6:
Rekod din da PREMIUM TIMES ta samu a Rumbun Tattara Bayanan Kidade (Open Treasury Portal), ya nuna cewa an daddatsa kudaden har gida 654, duk aka tura cikin asusun mutum 21.
Kashi 2 bisa 3 na kidaden duk mutum 2 aka tura wa su: Ogueri Ugochukwu Pascal da wani mai suna Olasehinde Micah.
An loda naira bilyan 1.6 asusun Pascal (N1,642,4407,539.93). Ba lokaci daya aka gabza masa kudin ba. Daddatsa kudin aka yi, aka rika tura masa har su 306.
Shi ma Micah an tura masa naira bilyan 1.4 (1,417,921,892.59). Shi kuma sau 34 aka tura masa kudaden.
Akasarin kudaden an tura su ne tare da bayanan abin da aka yi da kudaden. Amma bayanan daga na bige, gidoga sai na bad-da-bami.
Misali: An tura wa Pascal naira milyan 157 a ranar 26 Ga Oktoba, sai aka rubuta cewa kudin “rangadin neman kudin shiga ne na shiyya” da sauran dalilai da aka rubuta na logar Turanci mai kumbura wa mai karatu kai, yadda zai ga kamar wani gagarimin aiki ne aka yi da kudaden.
An danna naira milyan asusun wani mai suna Kamaru, har milyan 134.
PREMIUM TIMES ta kasa gano ko au wane ne Pascal da Kamoru.
Wasu da su ka samu na su rabon wannan watanda, sun hada Onwubalili Oyinlola, Nwaimo Obi Valenrine, Uzodinma Lucy Iquo; Oko Jaja Emmanuel, Waziri Mishella Micah. Kuma yawancin su duk daraktoci ne.
Akwai kuma jerin sunayen mutanen da aka kacalla wa kudaden, cikin su har da mai naira 583,200, wata mai suna Nafisa Yaro Ahmed.
Karya Dokar Hana Kudi Shiga Aljihun Ma’aikaci:
Abin da aka yi ya karya sashen Dokar Hada-hadar Kudade ta 7, Sashe na 701. Sannan kuma Doka Sashe na 713 ta jaddada kada a kuskura a yi haka, wato a kwashi kudin gwamnati a tura asusun ma’aikacin gwamnati.
An kuma gano an dankara wa wata mata mai suna Aishatu Audu Jauro naira milyan 13.5 domin “horas da ma’aikata.”
An dai gano cewa a shekarar 2019 an biya kudsden gwamnati har naira bilyan 51 a cikin asusun daidaikun mutane, wanda haka babban laifi ne a dokar kasa.
Jimillar kudaden da aka tura wa jama’a, alhali dokar kasa ta haramta irin wannan biyan kudade, sun kai naira bilyan 278. An raba kudaden ga mutum 5,000. Ko kuma a ce an tura kudaden sau 5,000.