BAYAN WATA DAYA: Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ya ki dakatar da wanda Buhari ya umarce shi dakatarwa

0

Wata daya cur bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustaoha ya dakatar da Babban Daraktan Hukumar PRODA, Charles Agulanna, har yau bai unarce shi ya fice daga ofis ba.

PREMIUM TIMES ta ji daga majiya mai tushe cewa Mustapha bai rattaba masa takardar dakatarwar ba, saboda shige-da-ficen masu nemar wa Shugaban PRODA din kamun-kafa janye dakatar da aka yi masa.

A ranar 9 Ga Oktoba ne Boss Mustapha ya nemi Shugaba Buhari ya amince ya dakatar da shugaban na PRODA har zuwa lokacin da za a kammala binciken zarge-zargen da ake yi masa, wadanda su ka kunshi “daddatsa kwangiloli, rashin zuwa wurin aiki ba tare da neman izni ba.

“Ana kuma zargin sa da nuna fifikon wata kabila a kan wata. Facaka da kudade da kuma zagon kasa.”

Masana halin da ake ciki sun tabbatar cewa har yanzu sakataren gwamnati Boss Musa bai dakatar da shi ba.

An ce Boss ya ki dakatar da shi ne saboda gudun kauce wa karya dokar Dokar COOAFRICAA ta 2004.

Sannan kuma takardar neman dakatar da Agulanna ta tabbatar da labarin da PREMIUM TIMES ta buga a cikin Yuli 2019, inda ya gano an harkalla a Hukumar PRODA.

Share.

game da Author