Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa dukkan masu hannu wajen kitsa zanga-zangar #EndSARS, wadda ta rikide ta zama tarzomar da ta haddasa kisa da asarar dukitoyi, za su dandana kudar abin da su ka aikata.
Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, lokacin da ake zantawa da shi a Gidan Talbijin na Channels, da dare a Abuja.
Shehu ya ce tabbas masu zanga-zangar dole su fuskanci shari’a.
“Kasar nan shugaba daya gare ta. Kuma kundin doka daya ta ke da shi. Buhari ne wuka da nama. Kuma komai na kan tebur din sa.
“Dokar kasa ta amince da zanga-zanga, amma idan ta wuce-gona-iri ta zoma tarzoma, to wannan kuma sai doka ta bi wa jama’a da kasa baki daya hakkin su.
” Kowa ya shaida irin mummunar barnar da aka yi aka daka wasoson kayan jama’a da na gwamnati, musamman a Lagos, Calabar, Filato, Taraba da wasu jihohi har da Abuja.
“To yanzu tilas mu kyale doka ta yi aikin ta. Ba ina magana ba ne kan wadanda su ka assasa zanga-zanga. Amma ina magana ne kan mummunar barnar da aka yi a Najeriya. Kuma wadanda su ka haddasa wannan barna sai sun gane kuskuren su.”
Shehu ya yi kira ga manyan jam’iyyun siyasa su fito su yi tir da tarzomar da ta barke din sanadiyyar zanga-zanga.
“Ina ganin ya kamata ‘yan Najeriya sama mikyan 200 su fito su ragargaji manyan ‘yan sisayar da su ka goyi bayan #EndSARS, tunda zanga-zangar ta rikide ta haddara mummunar tarzoma.
“Lallai tilas a ceto kasar nan. Jam’iyyar PDP kuma ya kamata ta fito ta yi tir da wannan mummunan abin assha da ya faru da sunan zanga-zanga.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Gwamnatin Najeriya ta yi wa kudaden masu zanga-zanga kamun-kazar-kuku a bankuna
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Babban Bankin Najeriya (CBN) iznin kulle asusun ajiyar wasu jagororin zanga-zangar #EndSARS da ke bankuna daban-daban.
Babban Bankin Najeriya ne ya nemi Mai Shari’a Mohammed Ahmed ya ba shi iznin kulle asusun bankunan na su, tun a ranar 20 Ga Oktoba.
PREMIUM TIMES ta ga wasikar da kotu ta tura wa Access Bank, Fedility Bank, First Bank, Guaranty Trust Bank, UBA da kuma Zenith Bank, inda aka umarce su kada su sake su bar masu asusun ajiyar a bankunan na su har su 20 su taba ko sisi cikin kudaden ajiyar na su.
Umarnin ya nuna cewa gwamnati na so ta yi amfani da kudaden da ke cikin asusun su a matsayin shaida.
Dalili kenan aka ce kada a bari su 20 din su taba kudaden ajiyar ta su, har sai bayan kwanaki 180, yadda kafin lokacin an kammala duk wani binciken da ya kamata a yi a kan su.
Wasu ‘yan gaba-dai-gaba-dai din #EndSARS da abin ya shafa sun hada da Bolatito Racheal Oduala, Chima David Ibebunjoh, Mary Doose Kpengwa, Saadat Temitope Bibi, Bassey Obi, Nicholas Ikhalea Osazele, Ebere Idibie, Akintomide Lanre Yusuf, Uhio Ezenwanyi Promise da Mosopefoluws Odesepe.
Sauran sun hada da Adegoke Pamilerin Yusuf, Umoh Grace Ekanem, Babatunde Vicror Segun, Mulu Louis Teghenan, Mary Oshifonawora, Winifred Akpevweoghene Jacob, Victor Solomon, Idunu Williams da Gatefield Nigeria Limited.