Ministan Harkokin ƴan sandan Kasa, Muhammed Dingyadi, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya lashe takobin ganin zanga-zangar #EndSARS bai sake faruwa a kasar nan ba.
Dingyadi ya bayyana haka ne bayan da aka kammala ganawar kwamitin tsaron Kasa da aka yi a fadar shugaban kasa, a Abuja, ranar Talata.
” Abinda gwamnati ke nufi a nan shine za ta cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma Ƙungiyoyi domin samun matsaya akan bukatun masu zanga-zanga da kuma cigaban kasa sannan da gujewa sake barkewar irin wannan zanga-zanga a kasar nan.
Dingyadi ya ce gabadaya shugaban hukumomin tsaron kasa sun garzayo fadar shugaban kasa ne domin yi masa bayanin halin da kasa ta ke ciki game da tsaro.
” An tattauna batun matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Gabas, inda shugaba Buhari ya umarci shugabannin tsaron su maida hankali matuka wajen kawo karshen wannan matsala.
Baya ga shugabannin hukumomin tsaron kasa da suka halarci taron, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Shugaban Ma’aikatan fadan shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da Sufeto Janar din Ƴan Sanda, Mohammed Adamu.
Discussion about this post