Babban bankin Najeriya ya ce babu inda saka Ajami a kudin Najeriya ya karya wani sashe na dokokin Najeriya.
Bankin ya maida wa wani lauya mai suna Malcolm Omirhobo martani kan korafin sa cewa wai rubutun Ajami da ke kudin Najeriya, karya dokar kasa sannan ya jibanta Najeriya da larabawa da kuma musulunci.
Lauya Malcolm Omirhobo, ya shigar da kara babbar Kotu a Legas yana kalubalantar saka rubutun Ajami da aka yi a kudin Najeriya.
Lauyan ya roki kotu ta tilasta wa bankin CBN ya cire wannan rubutu, tun da acewarsa wai Najeriya ba na musulmai bane su kadai kuma ba na larabawa bane.
Sai dai kuma, wakilin CBN, Abiola Lawal, ya bayyana wa kotu cewa wannan korafi na Omirhobo, ba abin da za a ma saurara bane.
Ya ce rubutun Ajami da ke kan nairorin Najeriya bai hada komai da larabci ba ko kuma musulunci ba.
Yayi bayanin cewa tun a wancan lokaci, an saka Ajami ne domin mutane su iya fahimtar darajar kudin da za su rika kashe ta yadda za su gane.
Jaridar Daily Trust ta buga wannan labari a shafinta.
Discussion about this post