Ba mu iya sa-ido kan kudaden shigar da gwamnati ke tarawa a asusun TSA – Akanta Janar

0

Ofishin Akanta Janar na Najeriya, wanda shi ne ofishin da ke bin-diddigin kudaden da gwamnatin tarayya ke tarawa da kashewa, ya ce ba shi da hali ko damar iya sa-ido kan kudin da gwamnatin tarayya ke tarawa a cikin Asusun Bai-Daya na Gwamnatin Tarayya (TSA).

Babban Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris ne ya bayyana haka a ranar Alhamis.

An kirkiro Asusun Bai-Daya, wato ‘Treasury Single Account’ (TSA), domin bin-diddigin kudaden da gwamnati ke tarawa da kashewa.

A baya, ma’aikatu da cibiyoyi da hukumokin gwamnati na bude asusun ajiyar makudan kudade a bankuna, ta yadda gwamnati ba ta ma sanin takamaimen yadda ake zarar kudaden da kuma yadda ake kashe su.

Amma bayan kirkiro TSA, sai gwamnati a cikin 2018 ta ce kirkiro Asusun Ajiyar na Bai-daya da aka yi, ya sa ana toshe satar naira bilyan 24 duk wata.

Sai dai kuma da ya ke ganawa da Kwamitin Harkokin Kudsde na Majalisar Dattawa, Akanta Janar Ahmed Idris ya ce duk da wadata da yawan na’urorin zamani da ake amfani da su a duniya, har yau ofishin sa ba ya iya bibiya, sa-ido, bin-diddigi ballantana sanin adadin kudaden shigar da ke shiga Asusun Bai-daya na gwamnatin tarayya, wato TSA.

An tambaye shi ko ofishin sa na da na’urorin sanin abin da ake tarawa kuwa, Idris ya ce babu.

Sai dai ya ce ofishin sa na cirar haraji ne daga hukumomin gwamnatin tarayya kai-tsaye daga asusun su, wanda kwamiti ya ce yin hakan haram ne.

Share.

game da Author