Gwamnatin Tarayya ta amince za ta biya Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) dukkanin albashin su na baya da na gaba ba ta hanyar tsarin IPPIS ba.
Ministan Harkokin Kodago da Ma’aikata, Chris Ngige ne ya bayyana wa manema labarai haka, a karshen ganawar da ya yi da shugabannin ASSU a ranar Juma’a.
Ngige ya ce za su duba batun ka’idar da gwamnati ta gindaya wa masu yajin aiki a baya, ta duk wanda bai je aiki ba, ba za a biya shi albashin rana ko watan da bai je ba.
Ngige ya ce gwamnati za ta duba wannan batun idan an zo biyan albashin baya.
Ya ce an cimma yarjejrniyar cewa za a biya albashin dukkan malaman da ba a yi masu rajistar IPPS daga Fabrairu zuwa Yuni 2020 ba, domin a biya su kudaden su.
“A taron, an kuma amince tsakanin Gwamnati da ASSU cewa za a tsara ka’idojin da za su warware matsalar da aka fuskanta wajen yi wa malaman rajistar IPPS a baya.
An ce Babban Akanta na Kasa, Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), sai Shugabannin Jami’o’i (Vice Chancellors).
Ngige ya kara da cewa gwamnati ta amince za ta biya ASSU tsohon albashin su na watan Fabrairu zuwa Yuni, ta hanyar bin tsohon tsarin biyan albashi, wato GIFIMS.
Sannan kuma ya ce an amince da zarar gwamnati ta samu kudi, za ta biya kashi 50 bisa 100 na kudaden inganta tsarin ilmi, har naira bilyan 110.
Batun alawus kuma da aka amince na naira bilyan 30, gwamnati ta amince za ta biya naira bilyan 25.
Akwai sauran kudaden alawus da gwamnati ta amince za ta biya na naira bilyan 40, ko kuma ta matse bakin aljihu ta biya bilyan 35.