Majalisar Dunkin Duniya (UN) ta bayyana cewa Arwacin Najeriya da kasashen Yemen da Kudancin Sudan za su fuskanci gagarimin rashin abinci da matsananciyar yunwa nan ba da dadewa ba.
Rahoton takamaimai cewa ya yi yankin Arewa maso Gabacin Najeriya ne zai fuskanci wannan yunwa. Ya kuma kara har da kasar Burkina Faso.
Hukumar Abinci ta Majalisar Dunkin Duniya (FAO) da kuma Hukumar Shirin Samar da Abinci ta Duniya (WFP) ne su ka fitar da wannan rahoto na hadin-guiwa.
Rahoton wanda bayan sun yi nazari su ka fitar a ranar Alhamis da ta gabata, ya bayyana cewa nan da watanni shida masu zuwa wasu kasashen 20 za su fuskanci tsananin yunwa da karancin abinci.
“Yemen, Sudan ta Kudu, Arewa maso Gabas a Najeriya da Burkina Faso akwai damuwa sosai, saboda yawan al’ummar yankunan kwata-kwata an datse su daga yadda za a yi su samu tallafi na agaji. Abin yanzu ya kai makurar tsananta, saboda shekarun da aka shafe ana fama da yaki a cikin yankunan.
” A wadannan yankuna, matsawa aka kai wasu watanni nan gaba ba a samu saukin yake-yake ba, to yunwa da rashin abinci za su kassara jama’ har ta kai wasu ga bingirewa.”
Daraktan Agajin Gaggawa na Hukumar Abinci ta Duniya, Dominique Burgeon ya ce wannan rahoto wani hannun-ka-mai-sanda ne da ya zama wajibi shugabannin wadannan kasashe su tashi tsaye, kuma su kwana cikin shiri.
“Muna bukatar samun sarari da za mu samu kutsawa cikin wadannan yankuna domin tabbatarwa su na da abinci, tare da halin noma abincin da zai kara masu lafiya, domin kauce wa barkewar yunwa.” Inji shi.
Ya ce bangarori hudu na duniya duk su na fama da wannan barazanar yunwa.
Dominique ta ce idan ba a manta ba, yunwa ta kashe mutum 260,000 a kasar Somaliya cikin 2011.
Idan ba a manta ba, a farkon makon jiya ne Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton cewa abinci zai gagari mutum milyan 22 a Najeriya nan da 2021.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin mai dauke da wani rahoto da Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta fitar, ya nuna cewa mutum milyan 22 na fuskantar barazana abinci ya gagare su nan da shekara ta 2000 mai zuwa.
Rahoton ya nuna cewa mutanen milyan 22 za su fara shiga garari ne tun daga watan Oktoba da ya gabata, zuwa Agusta 2021.
Rahoton mai suna ‘Cadre Harmonise’, an kaddamar da shi a Abuja ranar Alhamis, ya na dauke da nazari ne kan yiwuwar barkewar karancin abinci da karancin abinci mai gina jiki.
Rahoton ya ce mutane kimanin milyan 9 ne karancin abinci mai fara jefawa cikin garari tsakanin Oktoba zuwa Disamba, 2020.
Sannan rahoton ya ce mutum milyan 13 abinci zai gagara tsakanin watan Yuni, 2021 zuwa Agusta, 2021.
Wannan rahoto ya takaita bincike a jihohi 16 da su ka hada da Adamawa, Bauchi, Benue, Borno, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Plateau da Sokoto.
Sauran jihohin sun hada da Taraba, Yobe, Zamfara da Gundumar FCT, Abuja.
Wannan rahoto ya nuna yadda abin ya shafi jihohin Arewa ne, domin dukkan jihohin 16 a Arewa su ke.
Sakamakon binciken da CH ta fitar na makomar abinci a shekarar 2020, duk matsalar cutar korona ce taddasa shi.
Sabon rahoton da CH ta yi mai nuni da irin yadda abinci zai gagari mutum milyan 22, ya nuna duk da kowa ya koma harkokin sa bayan korona a Najeriya, to har yau milyoyin jama’a ba su kai ga warwarewa ba.
FAO ta ce a cikin 2020 ta raba wa gidaje 63,300 takin zamani da ingantaccen irin shukawa a cikin damina.
“An raba agajin tallafin kiwon dabbobi ga gidaje 12.000.”
Discussion about this post