An sace jami’an karban Haraji biyar a jihar Benuwai

0

Mahara sun yi garkuwa da wasu jami’an karban Haraji na jihar Benuwai a karamar Hukumar Vandeikya dake jihar.

Maharan dauke da bindigogi kuma sanye da kayan sojoji sun afkawa motan ma’aikatan ne a daidai suna wurin aika a karamar hukumar.

Isan su ke da wuya sai suka rika harbi ta ko-ina domin tsorata mutane daga nan sai suka diran wa motan ma’aikatan suka yi awon gaba da su.

Hukumar ta tabbatar da aukuwar wannan al’amari inda ta ce kafin maharan su tafi da ma’aikatan sai da suka ragargaza ofishin hukumar dake Vandeikya sannan suka kama gaban su tare da ma’aikatan.

Kakakin shugaban hukumara Ati Terkula, ya ce wannan abu ya faru ne da misalin karfe shida na yamma.

Share.

game da Author