An karrama Matawalle da kyautar gwarzon gwamna na 2019

0

Jaridar Sun ta karrama gwamnan jihar Zamfara da kyautar gwarzon gwamna na shekarar 2019.

Babban manajan kamfanin Jaridar Sun Onuoha Okeh, ne ya mika wa gwamnan kyautar a Gusau.

Okeh ya ce wannan karramawa ya zama dole ganin yadda gwamnan ya jajirce sannan yayi ta maza wajen ganin an samu raguwar kashe-kashe da zubda jinin mutane da jihar ta yi fama da shi a shekarun baya.

Bayan haka Okeh ya kara da cewa, ko da a mika sunayen mutane da dama a lokacin da ake tantancewa wanda za a ba wannan lambar girma, Matawalle ya zarce sauran a ma’aunin da aka saka su duka.

An duba bajintarsa da maida hankali da yayi wajen samar da tsaro a jihar, sannan kuma da bunkasa aikin noma da inganta rayuwar mutanen jihar da ya maida hankali akai.

A jawabin sa bayan amsar karramawar, Matawalle ya mika kyautar a madadin duk wadanda suka rasa rayukan sa a dalilin hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.

A karshe ya ce wannan karramawa ce ta kara masa kwarin guiwar cigaba da ayyukan samar da tsaro da yake yi a jihar da sauran ayyukan inganta rauwar mutanen sa.

Share.

game da Author