Gwamnatin jihar Delta ta bayyana cewa ashe cutar shawara ce ta yi ta kashe mutane a jihar a kwanakin baya, da aka y ta kokarin gano ko wacce irin cuta ce.
Gwamnati ta fadi haka be bisa ga Sakamakon binciken cutar da ma’aikatan kiwon lafiya ta gudanar.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya wata cuta da ba a san irin ta ba ta bayyana a jihar Delta inda ta kashe matasa masu shekaru 18 Zuwa 25, 30 a jihar.
Alamun wannan cuta sun hada da amai da jini, Suma, gudawa da dai sauran su. Cutar dai ta fi yin barna a karamar hukumar Ika Ta Arewa maso Gabas.
Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Mordi Ononye ya ce gwamnati ta tura ma’aikatan lafiya zuwa kauyukan da cutar ta bullo domin dakile yaduwar cutar.
Ononye ya ce an dauki jinin mutanen dake fama da cutar kuma an kai asibitin gwajin cututtuka dake Dakar kasar Senegal domin yin gwajin su.
Za a aiko da sakamakon gwajin nan da makonin biyu masu zuwa.
Bayan haka Ononye ya karyata yawan mutanen da cutar ta kashe a jihar wanda ake ta yayadawa.
Ya ce cutar ta kashe mutum 22 ne ba 30 ba kamar yadda wasu gidajen jaridu ke yadawa.
Ononye ya ce ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar da hukumar NCDC sun hada karfi da karfi domin ganin an dakile yaduwar cutar a jihar.
Discussion about this post