Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Frank Mba ya bayyana wa manema labarai cewa dakarun ƴan sanda sun ceto yan uwan su da masu garkuwa da mutane suka sace a Zamfara.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda mahara suka sace wasu ƴan sanda 12 a hanyar su ta zuwa Gusau aiki.
Mba ya ce dalilin da ya sa ƴan sanda suka yi shiru akai, shine don suna farautan maharan ne.
” Yanzu guda biyu na kwance a asibiti ana duba su, sauran kuma na nan garau.
Bayan haka Mba, ya ce sufeto janar din ƴan sanda Mohammed Adamu ua ce ƴan sanda za su ci gaba da aiki tukuru don ganin annkawo karshen hare-haren masu garkuwa da mutane a kasarnan.