Wani rahoto da Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta fitar, ya nuna cewa mutum milyan 22 na fuskantar barazana abinci ya gagare su nan da shekara ta 2021 mai zuwa.
Rahoton ya nuna cewa mutanen milyan 22 za su fara shiga garari ne tun daga watan Oktoba da ya gabata, zuwa Agusta 2021.
Rahoton mai suna ‘Cadre Harmonise’, an kaddamar da shi a Abuja ranar Alhamis, ya na dauke da nazari ne kan yiwuwar barkewar karancin abinci da karancin abinci mai gina jiki.
Rahoton ya ce mutane kimanin milyan 9 ne karancin abinci mai fara jefawa cikin garari tsakanin Oktoba zuwa Disamba, 2020.
Sannan rahoton ya ce mutum milyan 13 abinci zai gagara tsakanin watan Yuni, 2021 zuwa Agusta, 2021.
Wannan rahoto ya takaita bincike a jihohi 16 da su ka hada da Adamawa, Bauchi, Benue, Borno, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Plateau da Sokoto.
Sauran jihohin sun hada da Taraba, Yobe, Zamfara da Gundumar FCT, Abuja.
Wannan rahoto ya nuna yadda abin ya shafi jihohin Arewa ne, domin dukkan jihohin 16 a Arewa su ke.
Sakamakon binciken da CH ta fitar na makomar abinci a shekarar 2020, duk matsalar cutar korona ce taddasa shi.
Sabon rahoton da CH ta yi mai nuni da irin yadda abinci zai gagari mutum milyan 22, ya nuna duk da kowa ya koma harkokin sa bayan korona a Najeriya, to har yau milyoyin jama’a ba su kai ga warwarewa ba.
FAO ta ce a cikin 2020 ta raba wa gidaje 63,300 takin zamani da ingantaccen irin shukawa a cikin damina.
“An raba agajin tallafin kiwon dabbobi ga gidaje 12.000.”
Discussion about this post