Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta bayyana dalilan su na tafiya yajin aiki, tsawon watanni bakwai, kuma babu ranar komawa, duk kuwa da zaman tattaunawa da sulhuntawa da kungiyar ta sha yi da gwamnatin tarayya.
ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da yawan rashin cika alkawari, fada-ba-cikawa, tufka-da-warwara, rashin daukar abu mai muhimmanci da muhimmanci, “nuna rashin kunya da rashin mutunci ta hanyar rika shirya wa ASUU tuggu, manakisa, kutunguila, barazana da kirkira wa kungiya karya a idon jama’a, maimakon gwamnati ta yi da gaske wajen magance rikicin da ya tirnike da dadewa a tsakanin su.”
Wannan dalilai da ASUU ta bayyana su na cikin wata sanarwar da Shugaban ASUU na Shiyyar Lagos, Olusiji Sowande ya fitar a ranar Litinin.
Batun Rashin Cika Alkawari:
Daga cikin dalilan akwai kuma rashin cika alkawarin yarjejeniyar shekara ta 2009 da aka kulla gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (FGN-ASUU).
Wannan yarjejeniya ce da aka yi cewa gwamnatin tarayya ta wadatar da kudaden gyaran dukkan gine-ginen da su ka lalace a cikin jami’o’i, da su ka hada da dakuna da gidajen kwanan dalibai, manyan zauruka ko ajujuwan karatu, dakunan binciken dabarun harhada magunguna da kuma samar da yanayi mai kyau na jin dadin koyarwar malaman jami’o’i.
“Akwai kuma batun biyan malamai alawus da Cancantar Koyar da Darussa (EAA), sai kuma kafa kwamitin da zai rika kai ziyara a jami’o’i domin sa-ido da tabbatar da ana gudanar da ayyukan kamar yadda su ka dace a yi.” Inji Sowande.
Sowande ya ce Gwamnatin Tarayya ta shigo ko ta kirkiro batun biyan albashi da tsarin IPPIS a jami’o’i ne kawai domin da karkatar da jama’a daga dimbin alkawurran da ta kasa cikawa a baya.
Ya ce “saboda rashin mutunci sai gwamnati ta rike albashin malaman jami’o’i a lokacin zaman gida saboda korona, a bisa dalilin wai mun ki bin tsarin IPPIS.”
Ya ce jama’a su sani gwamnatin tarayya ta rike wa malaman jami’o’i alhashin watanni hudu, daga Yuli zuwa Oktoba.
“Akwai wadanda ma kamar a Jami’ar Maiduguri, Jami’ar Nazarin Aikin Noma ta Michael Okpara da ke bin albashi har da na watan Fabrairu zuwa Yuni.”
Sowande ya yi zargin cewa ana shirya gagarimar harkalla, ana sace makudan kudade a Ofishin Akanta Janar na Tarayya da sunan IPPIS, tare da hadin bakin Ma’aikatar Kudi ta Tarayya.