4-4: Yadda ƴan wasan Saliyo su ka kunyata Super Eagles a Najeriya

0

Ƴan wasan Najeriya sun tattaru garin Benin, babban birnin jihar Edo cikin nishadin kafsawa da kungiyar kwallo ta kasar Saliyo, tare da yi masu rugu-rugu, a filin wasan da babu ‘yan kallo.

Sai dai kuma duk da ‘yan wasan na Najeriya sun rugurguza wa Saliyo kafafu da cin kwallaye hudu, an kwashi buhun kunya yayin da Saliyo ta farfado bayan sun sha ruwa a hutun-rabin-lokaci.

Kwallaye 4 da Najeriya su ka kwarara a ragar Saliyo sun koma tubalin toka, bayan Saliyo ta rama kwallayen ta 4 cif bayan an koma hutun-rabin-lokaci.

Yayin da Alex Iwobi, Victor Osimhen da Samuel Chukwueze su ka jefa kwallaye 4 a ragar Saliyo, Kwame Quee, Hadji Kana da Mustafa Bundu sun rama wa Saliyo kwallayen ta duka.

Takaici ya zama biyu ga Najeriya yayin da dan wasan da ta fi ji da shi, Victor Isimhen ya ji rauni a wasan, wanda ci gaba ne na share fagen wadanda za su buga gasar cin Kofin Afrika.

A yanzu Najeriya ta na da maki 7, Saliyo 2.

Share.

game da Author