Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 155 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –60, Katsina-37, Kaduna-35, FCT-6, Ogun-4, Edo-3, Kwara-3, Rivers-2, Kano-2, Jigawa-1, Oyo-1, Taraba-1.
Yanzu mutum 66,383 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 62,076 sun warke, 1,167 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,140 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 22,962, FCT –6,498, Oyo – 3,703, Edo –2,694, Delta –1,823, Rivers 2,956, Kano –1,773, Ogun –2,153, Kaduna –2,895, Katsina -1,007, Ondo –1,727, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi – 753, Ebonyi –1,055, Filato -3,800, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –662, Jigawa – 328, Kwara –1,091, Bayelsa – 445, Nasarawa – 485, Osun –945, Sokoto – 165, Niger – 295, Akwa Ibom – 319, Benue – 493, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 92, Ekiti – 353, Taraba- 157, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Annobar Korona a Afirka
Annibar Korona na cigaba da yaduwa a Nahiyar Afirka wanda zuwa yanzu alkaluma suka nuna cewa sama da mutum miliyan biyu sun kamu da cutar.
Mutum sama da miliyan 1.7 sun warke sannan mutum 48,000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
Ofishin WHO dake Brazzaville kasar Kongo ya sanar da haka.
Zuwa yanzu kasashen Afirka ta Kudu, Algeria da Kenya ne kasashe a nahiyar da suka fi kamuwa da cutar.
Kasar Afrika ta Kudu mutum 757,144 sun kamu, 20,556 sun mutu.
A Algeria mutum 70,629 sun kamu, 2,206 sun mutu.
Kasar Kenya ta samu mutum 72,686 da suka kamu da mutum 1,313 da Suka mutu