2023: Ku fito a fafata da ku a siyasa – Kiran gwamnati ga matan Katsina

0

Gwamnatin jihar Katsina ta yi kira ga matan jihar da su fito suma a fafata dasu a fagen siyasar jihar a 2023 idan Allah ya kai mu.

Kwamishinan harkokin mata Rabiatu Muhammad-Daura ta yi wannan kira da take zantawa da manema labarai a garin Katsina.

Rabiatu ta ce ma’aikatar harkokin mata za ta gudanar da tarurruka domin wayar wa mata kai sanin mahimmancin fadawa tsindum cikin harkokin siyasa da gwamnati.

Ta ce abin takaici ne yadda ace a duk fadin jihar babu mace daya da take wakiltan jihar a majalisar dokokin jihar ko majalisar Tarayya.

Rabiatu ta ce gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa mata domin su zama masu cin gashin kansu.

Tallafa wa mata na daga cikin ayyukkan inganta rayuwar mutane da gwamnatin jihar ke yi a jihar.

Bayan haka Rabiatu ta ce a cikin wannan shekara da muke ciki, gwamnati ta tallafa wa mata 34,000 a jihar da murhun dake aiki da iskar gas sannan ta hada wasu da dama da hukumomin da za su iya samun bashi domin samu jarin yin sana’a.

Ta Kuma ce ma’aikatar su za ta maida hankali wajen kawar da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi da ya kazanta a tsakanin mata a jihar.

Share.

game da Author