Dan majalisan dake wakiltar mazabar Kabba-Bunu/ Ijumu na jihar Kogi a majalisar wakilai ta Tarayya Tajudeen Yusuf ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bude asibitin FMC a jihar.
Yusuf yace buɗe wannan asibiti zai taimaka wa mutane jihar matuka musamman a wannan lokaci da jihar ke karancin manyan asibitoci.
Yusuf ya yi wannan roko ne a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Lahadi a garin Lokoja.
Ya ce rufe asibitin da gwamnati ta yi ya jefa mutane cikin halin ƙaƙanikayi da har mutuwa mutane ke yi a dalilin rashin asibitin.
“Saboda rashin asibiti irin FMC marasa lafiya a jihar sai sun yi dogon tafiya zuwa Abuja ko Ibadan idan ciwo yayi tsanani domin zuwa manyan asibiti.
Yusuf ya ce gwamnati ta rufe wannan asibitin ne bayan wasu ‘yan iskan gari sun far wa asibitin inda suka lalata kayan aiki sannan suka yi awon gaba da wasu.
Sannan da matsalar kwantar da wani limamin masallacin Kabba Abubakar Ejibunua da aka yi a asibitin wanda hukumar NCDC ta tabbatar ya kamu da cutar korona.
Gwamnatin ta ki amincewa da sakamakon gwajin cutar da hukumar NCDC ta gabatar cewa hukumar ta gudanar da gwajin batare da sanin jami’an lafiya dake jihar ba.
Yusuf ya yi kira ga ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya yi amfani da ikon sa ya bude wannan asibiti a jihar.
Ya ce bai kamata laifin wani ya shafi miliyoyin mutanen da basu san hawa ba ba su san sauka ba.
Discussion about this post