Ƴan sandan Najeriya sun cafke wasu cikin tsirarun masu zanga-zanga 4 a Abuja ranar Juma’a da safe.
Wasu masu zanga-zangar # EndSARS sun fito domin ci gaba da yin zanga-zanga a Abuja ranar Juma’a.
Karkashin jagorancin mawallafin Sahara Reporters, Yele Sowore, madu zanga-zangar sun yi dafifi a kofar shiga majalisar Kasa suna kira da a soke rundunar SARS.
Sai dai kuma masu zanga-zangar sun koka kan cewa ƴan sanda sun ci zarafin su a wannan wurin Zanga-zanga.
” Muna zanga-zangar mu salin-alin, kwatsam sai ƴan sanda suka afka wana suna ta jejjefa mana barkonon tsohuwa sannan suka fatattake mu. Ni har an bata min mota.” Inji Sowore.
Dama kuma a baya rundunar ta gargadi masu niyyar sake fitowa zanga-zangar # EndSARS su cewa kada su kuskura su sake fitowa titina.
Sai dai wanna kira bai yi tasiri a kunnuwan su ba.
Discussion about this post