Jami’in yada labarai na Kwalejin Kimiyya da Fasaha, ‘Nuhu Bamalli Polytechnic’ dake Zariya, Abdulallahi Shehu ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, cewa mahara sun sace wani malamin kwalejin da yaran wani malamin daban ranar Lahadi.
A cikin zantawar da yayi ta wayar tarho da wakilin NAN, shegu yace dukkan su da aka sace na zaune ne a harabar kwalejin, wato gidajen su na harabar kwalejin ne.
Ya kara da cewa shi wannan malami da aka sace yana koyarwa ne a sashen koyar da fasar kere-kere dake Kwalejin.
Yace su kuma wadannan yaran biyu da aka sace ƴaƴan wani ma’aikacin Kwalejin ne da ke zaune a kwalejin.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Mohammed Jalige ya tabbarar da aukuwar wannan al’amari, sannan ya ce tuni har an tura jami’an ƴan sanda domin su fantsama yin farautar maharan da kuma ceto wadanda suka yi garkuwa da su.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Arewa masu Yamma da ke fama da hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane.
Discussion about this post