Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya, UNICEF sun yi kira ga kasashen duniya su mike tsaye wajen yaki da cututtukan bakon dauro da shan Inna a kasashen su.
Kungiyoyin sun yi wannan kira ne ganin yadda Korona ta dakatar da gudanar da harkokin rayuwa yadda ya kamata, musamman a fannin kiwon lafiya.
Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya ce a dalilin bayyanar cutar korona kasashen duniya da dama ba su iya tafiyar da aikin yi wa yara allurar rigakafi inda hakan ya sa cututtukan dake kisan yara kanana suka cigaba da yaduwa.
Ghebreyesus yayi kira ga kasashen duniya da su yi amfani da ilimi da matakan kawar da wadannan cututtuka da suke da su domin ceto rayukan yara a kasashen su.
WHO da UNICEF sun ce ana hasashen cewa cutar Shan Inna zai yadu a kasashen Pakistan da Afghanistan da wasu kasashen Afrika.
Hanyoyin inganta yi wa yara allurar rigakafi
Shugaban asusun UNICEF Henrietta Fore da wakilin UNICEF a Najeriya Peter Hawkins sun ce ya zama dole gwamnatocin kasashen duniya su maida hankali wajen yi wa yara allurar rigakafin cututtukan dake yin ajalinsu musamman awannan lokaci da komai ya karkata ne wajen yadda za a dakile yaduwar cutar Korona.
Henrietta da Hawkins sun ce gwamnatocin kasashen duniya za su samu nasarar yin haka ne idan suka ci gaba da wayar wa mutane kai kan sanin mahimmancin yi wa yara allurar rigakafi.
Sannan da ware isassun kudade domin siyo magungunan da za a bukata, karkato da hankulan sarakuna da malaman adddini su taimaka wa gwamnati a wajen yaki da cututtukan da sauran su.
Discussion about this post