Ƙungiyar Kare ƴan Jarida ta Duniya (CPJ), ta karrama mawallafin PREMIUM TIMES, Dapo Olorunyomi da Lambar Kyautar ƴancin ƴan Jarida ta Duniya (IPFA), saboda jajircewar sa wajen rike gaskiya da fallasa harkalla a Najeriya da duniya, sai kuma yadda gurungundumar kuntatawa da ya rika fuskanta a hannun masu mulki da jami’an tsaro, ba ta sa ya sassauta ba.
An karrama Dapo tare da wasu mashahuran ƴan jarida uku na duniya da su ka fito daga kasashe daban-daban.
Wadanda su ka shirya bada kyautar yabo da jinjinar, sun bayyana cewa dukkan su hudun sun sha gwagwarmaya da fuskantar tuhuma daga gwamnatocin kasashen su, saboda yawan wallafa rahotonnin da ba su yi wa mahukuntan kasashen dadi ba.
Sun bayyana cewa Dapo ya cancanci jinjina a duniya, saboda shekaru sama da 20 da ya shafe wajen gwagwarmayar samar wa ƴan jarida da hakkin jarida ƴanci a Najeriya, duk kuwa da irin rintsi da hatsarin da ya rika fuskanta a rayuwar sa.
An taba kama shi sau biyu a zamanin mulkin soja na Janar Sani Abacha, cikin 1995. Tura ta kai shi bango inda ya samu sararin tsallakewa zuwa gudun-hijira a Amurka.
Baya-bayan nan ma a cikin 2017, jami’an ƴan sanda sun je har babban ofishin PREMIUM TIMES na Abuja sun kama shi, a kan zargin bata suna.
“Wannan lambar yabo ta tunatar da ni, kuma na yi imani ta tunatar da abokan aiki na ƴan jarida masu yawa cewa, akwai sauran aiki gagarimi wajen bunkasa aikin jarida, yadda zai kara bankado hakikanin gaskiyar irin yadda dimkoradiyyar mu ta ke.”
Haka Dapo ya furta a cikin jawabin sa a lokacin da ya ke karbar ta sa lambar yabon.
Sauran wadanda aka karrama su tare, sun hada da Shahidul Alam, gogaggen dan jarida daga kasar Bangladesh, sai Mohammed Missed daga Iran da kuma Svetlana, ‘yar kasar Rasha.
Alam mai daukar hoto ne da ya yi shaharar da ta kai shi shafe kwanaki 102 a kulle, cikin shekarar 2018, saboda ya watsa bidiyon da aka nuno dalibai na zanga-zanga a Dhaka, babban birnin kasar Bangladesh.
Shi kuma Mosaed na Iran, zakakurin dan jarida ne mai zaman kan sa, wanda irin labaran harkallar da ya rika fallasawa, sai da su ka ja masa daurin shekaru hudu a kurkuku.
Bayan ya fito, bai daddara ba, ya ci gaba da abin da ya saba, har aka sake kama shi sau biyu.
Ita kuwa Prokopyeva ‘yar kasar Rasha, ma’aikaciyar wani gidan radiyo ce, Radio Svoboda, wadda ko cikin 2019 sai da jami’an tsaron Rasha su ka kai wa gidan ta hari, su ka kwashe kayan aikin ta da wasu kayan amfanin ta na yau da kullum, kuma su ka garkame ta.
Ko a cikin watan Nowamba din nan, an yanke mata tarar biyan dala 6,980.