Zanga-Zangar #EndSARS ya rikide ya koma na tashin hankali – Lai Mohammed

0

Ministan Harkokin Yada Labarai ya koka kan yadda masu zanga-zangar #EndSARS suka canja salon zanga-zangar zuwa na tashin hankali da tambadewa.

Lai Mohammed ya gargadi masu zanga-zangar da su shiga taitayin su domin gwamnati baza ta zuba musu ido ba suna neman su kawo rudani a kasar nan.

” Ku duba ku gani da karfin tsiya suka shiga kurkukun Edo, suka saki fursoni da dama. Bayan haka kuma suna takura wa mutanen kasa da kawo rudani a duk inda suke.

” Ko a yau Litinin, mun samu rahoton wani daga cikin jagororin wannan zanga-zanga da ya ce ya janye daga zanga-zangar saboda wasu daga kasashen waje sun yi kane-kane a ciki.

” Ya ce wasu ne daga can suke turo wa masu zanga-zangar kudade domin su cigaba da zanga-zangar, amma ba yadda suka tsara zanga-zangar tun farko ake yi ba.

Lai Mohammed ya ce bayan haka kuma wasu kungiyoyi da ke cikin wadanda suka shirya zanga-zangar tun a farko duk sun cire hannayen su a ciki saboda jagwalgwalon da ta zama yanzu.

Ƴan kasuwa da masu sana’o’in musamman a jihar Legas duk sun shiga halin ha’ula’i a dalilin masu zanga-zanga bayan kuma dama har yanzu ana kokarin farfadowa ne daga tabarbarewar arzikin da Korona ta jefa kasashen duniya a ciki.

Share.

game da Author