Zanga-zangar #EndSARS ‘wata makarkashiya’ ce – APC

0

Shugaban Rikon Jam’iyyar APC na Kasa, Mala Buni, ya bayyana cewa idan ba da gaske aka yi ba, to zanga-zangar #EndSARS za ta iya jefa kasa nan yamutsin bijire wa doka.

Buni wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Yobe, akwai wata boyayyar manufa a kunshe cikin zanga-zangar #EndSARS, wadda ta yi sanadiyyar rasa rayuka a kasar nan.

Ya shaida wa BBC Hausa cewa akwai bukatar shugabanni masu a fada-a-ji su sa baki, su yi wa masu zanga-zanga magana su lallashe su su janye jiki daga kan titinan kasar nan, gudun kada zanga-zangar ta kai ga rikidewa zuwa kazamar tarzoma.

Fargabar Bazuwar Tarzoma:

“Batagari na iya amfani da wannan dama, su fake da zanga-zanga su fantsama kazamar tarzoma. Domin irin yadda zanga-zangar ta sauya salo a yanzu, ta nuna akwai boyayyar manufa tare da lamarin.”

“Ya kamata mu yi hattara. Najeriya cike ta ke da mutane masu ra’ayi daban-daban. Wani so ya ke yi a sake fasalin Najeriya, wasu kuma bukatar su kawai ita ce Najeriya ta tarwatse.” Inji Buni.

Ya kara da cewa, “ai akwai masu aikata muggan laifuka da ke kallon SARS wata barazana ce ga mummunan ayyukan laifin da su ke tafkawa.

“Har yanzu kalubalen da ke gaban Najeriya su na da yawa. Gwamnatin Buhari ba ta iya shawo kan wadannan matsalolin a cikin shekarun 5. Kasar da a baya wasu ‘yan kakuduba su ka sace dala bilyan 16 tashi daya, a ce har yanzu ba ta durkushe ba, a sani wannan aikin addu’o’i, amma ba wani tsimi ko wata dabara ba.” Inji Buni.

Share.

game da Author