Kifi na ganin ka mai jar koma muke yiwa ƴan kudancin Najeriya. Sun yi nutso ne muna ganin bayan su. Suna yi mana kallon biri, mu kuma muna yi musu kallon ayaba. Mun fita daga cikin gidadancin da suke kallon mu da shi a shekarun baya.
Idan har gwagwarmaya suke yi don gyaran Najeriya, dole sai matsalolin mu sun zama nasu, muma nasu sun zama namu. Amma tunda ake fama da matsalar tsaro a Arewacin Najeriya basu taba goya mana baya ba saboda gani suke yi ba matsalarsu bace. Matsalar ƴan Arewa ce kawai.
Sai kuma daga baya muka ji sun fito da tafiyar ‘#EndSARS wacce suka boye manufofinsu daga farko. Amma yanzu gasu sun fara bayyanasu. Kar muke kallonsu da idon basira. Don ba gidadawa bane ba mu, waďanda za a busa kahon farauta kawai su fito.
Duk “Zanga-Zanga” da ake yi a duk fadin duniya, mun sani kuma mun gani, idan aka biya masu buƙatunsu daina wa suke yi. Saboda sun cimma burinsu amma duk sanda hakan bata yiwu ba, to gaskiya an fake da guzuma ne don a harbi karsana.
Zanga-Zangar #EndSARS ba a kan SARS bane kawai, muna zargin ƴan ‘revolution’ ne suke so su yaudari mutane don biyan bukatarsu. ‘Yan kudancin Najeriya sun mayar da sabgar kamar rigima da Arewa.
Shi yasa duk inda kaga ana yi, to da wuya ka samu matasa cikakkun ‘yan Arewa. Ko wanda aka yi a Sabongari ta Kano, ba cikakkun Kanawa bane. Sun mayar da abun na yankin da mutum ya fito.
Idan kana so ka tabbatar da maganata, tafi ka duba duk wata jarida da take kan dandalin sada zumunta. Madadin a samu haďin kai tsakanin matasa ‘yan kudu da na Arewacin Najeriya, ban da cin mutuncin juna babu abunda suke yi, saboda sun nuna kamar suna faďa ne kawai da mulkin ‘yan Arewa. A lokacin Obasanjo da Goodluck basu taba irin wannan yinkurin ba.
Najeriya ‘Republic’ ce, ba zai yiwu wani bangare yace baya so ďaya bangeren ya mulke shi. Tunda Allah ya haďamu waje ďaya dole sai mun yi hakuri da juna. Amma shekara da shekaru hakan yaki yiwuwa saboda hassada.
Ina baiwa matasan Arewa shawara da su janye jikinsu daga zanga-zangar karya.
Allah ya kiyaye.
Discussion about this post