Shugaban Rikon Hukumar Hukumar Dakile Wawurar Kudade da Ayyukan Zamba (EFCC), ta bayyana cewa duk da tsaikon gudanar da wasu ayyuka da barkewar konana ta haddasa, EFCC ta gurfanar da mutum 646 a kotu kuma ta kwato kadarorin da kudin su sun kai naira bilyan 10 a cikin 2020.
Shugaban Rikon EFCC Umar Abba ne ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Kula Laifukan Zamba da Wawurar Kudade, a ranar Talata, a Abuja.
Kakakin Yada Labarai na EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce Majalisar Dattawa ta nuna shauki da bukatar ganin an samu sauyin tafiyar da tsare-tsaren EFCC, domin a kara wa yaki da zambar kudade da kwato kudaden sata karfi sosai.
Shugaban Kwamiti Sanata Sulaiman Kwari, ya bada shawara cewa kamata ya yi kafin EFCC ta kama wanda ta ke zargi, to ta tabbatar ta yi akalla kashi 90 bisa 100 na binciken da ya kamata ta yi masa.
Ya kuma yi kira da EFCC ta daina bulkara da buyagi a jaridu. Ya na mai cewa idan EFCC za ta yi aiki, to ta yi aikin ta kawai, sai jama’a su gani kuma su jinjina wa hukumar, maimakon tun ba ta kammala bincike ba ta yi ta kwakwazo a kafafen yada labarai.
Mataimakin Shugaban Kwamiti, Sanata Aliyu Wamakko, ya yi korafin cewa kudaden da EFCC ke biyan lauyoyin ta sun yi kadan.
Ya ce matsawar ana son samun kwararrun lauyoyin da za su rika yin aiki nagari a kotunan da EFCC ta gurfanar da wadanda ta ke kamawa, to ya zama wajibi a kasafin EFCC a kara wa lauyoyin da ke wakiltar hukumar kudaden ladar aiki.
Da ya ke bayani, Umar Shugaban EFCC ya nuna damuwa dangane da tulin motocin da hukumar ta kama, wadanda ke zube, har wasu na neman lalacewa.
Ya ce ba a motoci kadai a ke da wannan matsalar ba. Akwai gidaje da gine-gine masu tarin yawa da ke a hannun EFCC, kuma ba a sayar da su sun zama kudi ba.
Ya ce ya na fatan Ministan Shari’a Abubakar Malami zai fito da tsarin da ya dace a yi gwamjon kadarorin.