ZABEN ONDO: Za a baza ‘yan sanda 33,783 -Sufeto Janar Adamu

0

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa za ta tura jami’an ta 33,783 zuwa cikin Jihar Ondo, domin su tabbatar da cewa an gudanar da zaben gwamna da za a yi ranar 10 Ga Oktoba lami lafiya.

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Adamu ne ya bayyana haka.

Adamu ya yi wannan bayani a Akure, bababn birnin Jihar Ondo, a lokacin da ya ke ganawa da masu ruwa da tsaki a zaben, da su ka hada da jam’iyyun siyasa, sarakunan gargajiya, masu sa-ido kan zabe da sauran su, a ranar Litinin.

Ya ce za a tura game-garin ‘yan sanda 30,933 sai kuma ‘yan sandan musamman 2,850.

Adamu ya kara da cewa baya ga wadannan tulin ‘yan sanda da za a tura, akwai kuma gamayyar jami’an tsaro har 3,500 daga sauran bangarorin tsaro na kasar nan daban-daban.

“Za a jibge sojoji domin tsare kan-iyakokin jihar, su kuma sojojin sama za su rika shawagin sintiri daga sama.

“Za a wadatar da jami’an tsaron domin kare rumfunan zabe 3,009, mazabu 203 da ke cikin Kananan Hukumomi 18 na Jihar Ondo.

“Aikin su shi ne su tabbatar sun tsare jami’an zabe da kuma kadarorin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC). Kuma su tsare lafiya, rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Ondo, kafin ranar zabe, ranar zabe, lokacin zabe da kuma bayan kammala zabe.” Cewar Adamu.

Ya ce za a turo su da yawa ne domin tabbatar da cewa wasu manya da kananan batagarin ‘yan siyasa da ‘yan jagaliya ba su dagula ko hargitsa zaben ba.

Ya ce za a tabbatar an gudanar da zabe daidai da yadda Dokar Zabe ta Kasa a karkashin INEC ta shimfida.

Ya ce wannan kuma gargadi ne da jan kunne ga duk wani takadari da mai kunnen-kashi cewa jami’an tsaro ba za su sassauta wa duk wani da ya nemi kawo kafar-ungulu wajen ganin ya hana gudanar da zabe lami lafiya ba.

Adamu ya ce za a kama mutum a gurfanar da shi.

Share.

game da Author