Dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar ZLP, kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya karyata rade-radin da ake cewa ya janye takarar gwamna da ya ke yi.
Ana ta watsa ji-ta-ji-ta a jihar cewa a yau Asabar Ajayi ya bayyana janyewa daga takarar sa a karkashin ZLP.
Sai dai a cikin wata sanarwa da daya daga cikin hadiman sa, Allen Sowore ya fitar, Agboola ya ce ji-ta-jitar duk sharri ne da tuggun ‘yan jam’iyyar APC.
“Na samu labarin wai ana watsa takardar da na yi sanarwa cewa na janye daga takarar gwamna a karkashin ZLP. Wannan kuwa duk zancen banza ne.
“Gwamna Rotimi Akeredolu da APC ba za su taba gajiya da yayata karairayi a kai na ba. Yanzu ma ga ta nan shi da kakakin yada labaran sa sun shirga min wata karyar ana watsawa.
” Wannan karyar da su ka shirga min fa ba ta da wani bambaci da waccan karya da su ka yi min a baya wai na hada kai da jam’iyyar PDP. Wannan duk sharrin Akeredolu ne, gwamna mai barin gado.” Inji Ajayi.
Sai dai kuma kakakin na Ajayi bai kawo wata hujja da ta nuna cewa APC ce ta kitsa ji-ta-ji-tar ba.
INEC dai ta ce Ajayi da ZLP duk su na cikin masu takara.