ZABEN ONDO: An dambace a wajen rabon kudi a Idanre

0

Masu zabe sun kaure da kokuwa a tsakanin su wajen rabon kudin ‘Yan siyasa a Idanre.

Wakilin mu da aka yi abin a idon sa ya bayyana cewa wasu sun kasa hakuri rabon ya iso kan su. Sun rika mangare mutane sun naushe-naushe domin su kaiga wajen samun nasu rabon.

‘Yan PDP sun ce abin har da nuna rainin wayau, domin kiri-kiri zaka ga mutum kafin ya jefa kuri’a sai ya dan karkata takardar zaben domin wani a gefe ya tabbatar APC ya dangwala wa APC ne, daga nan sai ya amshe kudin sa ya cake ya kara gaba.

A dalilin haka ne fa sauran jam’iyyun suka ce ba za ta sabu ba, suma suka shiga cikin yamutsin da kuma yin kira ga jami’an zabe su dakatar da zaben ko kuma su hargitsa shi.

idan ba a manta ba Rundunar ‘Yan Sandan Ondo ta bada sanarwar cewa ta damke jami’in ta daya, bayan ya karya dokar zaben da ta haramta wa dogaran manyan masu mulki su janye daga raka su zuwa wurin dangwala kuri’a.

An kama dan sandan bayan ya raka Alaba Lad-Ojomo zuwa dangwala kuri’a a Mazabar Owo, cikin Karamar Hukumar Owo.

Alaba ya taba yin Dan Majalisar Tarayya har sau biyu. Kuma har yanzu ba a bayyana suna da mukamin dan sandan ba.

A lokacin da wakilin mu isa wurin, ya iske ana ta markabu, shi kuma Lad-Ojomo na ta rokon wani babban jami’in dan sanda cewa ya saki dogarin na sa.

Sai dai a gaban wakilin mu babban dan sandan ya ce, “ba zan sake shi ba. Saboda ya yi rashin da’a.”

Daga nan Lad-Ojomo ya fusata, ya rika zazzafar cacar-baki da babban dan sandan. A karshe ya bar wurin cikin fushi, ganin cewa an ki sakar masa dogari.

Lad-Ojomo ya yi majalisar tarayya a zaben 2003 da 2011. Daga nan kuma ya yi ta kokarin zama shugaban jam’iyyar PDP a jihar Ondo a 2020.

Wani da aka yi abin a gaban sa, amma ba ya so a ambaci sunan sa, ya ce, “dan sandan da aka damke din ya cika girman kai da fankama da tinkaho.”

Share.

game da Author