Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a samu gibin naira tiriliyan 4.28 a Kasafin 2021.
Da ya ke bayanin yadda za a cike gibin, Buhari ya shaida wa gamayyar majalisin Dattawa da Mambobin Tarayya cewa bashi za a ciwo domin a yi wa al’umma ayyukan raya kasa, saboda kudaden shigar da Najeriya ta yi hasashen tarawa, ko kadan ba za su isa a yi manyan ayyukan da su ka kamata a yi da su ba.
Buhari ya ce cikin 2021 za a kashe naira bilyan 501.19 wajen biyan kudaden fanshon tsoffin ma’aikata.
Ya ce za a kashe naira tiriliyan 3.124 wajen biyan basussukan da su ka yi wa Najeriya katutu.
Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta (NDDC) za ta samu naira bilyan 63.51. Hukumar Farfado da Yankin Arewa maso Gabas za ta samu naira bilyan 29.70, sai Hukumar Bunkasa Ilmi a Matakin Farko (UBE) ta za samu naira bilyan 70.
Za a bai wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) naira bilyan 40, sai Majalisun Dattawa da ta Tarayya naira bilyan 120.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana yadda aka cimma shata hasashen kashe naira tiriliyan 13.08 a Kasafin Najeriya na 2021.
Wannan ne karo na shida da Buhari ya gabatar da kashe kasafin shekara-shekara tun bayan hawan sa mulki a 2015.
Ya gabatar da na 2016, 2017, 2018, 2019 da kuma na 2020 a shekarun baya a jere.
Kasafin wanda aka rada wa suna, “Kasafin Fardado Da Tattalin Arziki”, Buhari ya ce an tsara shi a matsayin sharar-hanyar kudirin gwamnatin sa na bunkasa tattalin arzikin Najeriya a karkashin Shirin NDP 2021 – 2025.
Ya ce an kintacen farashin gangar danyen man fetur a kan dala 40, wanda akan wannan ma’auni ne aka yi kasafin dungurugum.
Sannan ya kara da cewa an sake auna ma’aunin a kan kowace dala daya daidai da naira 376.
Ya ce an yi kasafin a bisa hasashen za a rika hako danyen mai ganga milyan 1.86 a kowace rana.