Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), ta bayyana cewa ta rattaba hannun amincewa da dukkan bukatun masu zanga-zangar #EndSARS, kuma za ta magance ko biya musu bukatun domin kara wa gwamnati karsashin gudanar da ingantaccen mulki da gwamnati.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da NGF din ta fitar ranar Litinin.
Makonni biyu kenan a kullum masu zanga-zanga na ci gaba da jerin gwano, mamaye manyan titina a Lagos, Abuja da sauran jihohi da dama.
Ko a ranar Litinin din nan masu zanga-zanga sun fita a Kaduna da Kano.
A Abuja kuma sun yi kwanan-zaman-dirshan a bakin harabar Babban Bankin Najeriya (CBN).
Zanga-zangar dai ta rikita harkoki ta kuma tsayar da hada-hada da ayyukan gwamnati a wasu wurare.
Ta kara muni ganin yadda kawowa ranar Litinin mutum 12 ya rasa ran sa a wurin zanga-zanga.
Gwamnatin Tarayya ta amince ta biya wa masu zanga-zanga dukkan bukatun su biyar da su ka nema.
Gwamnoni Sun Yunkuro:
Gwamna Fayemi ya ce gwamnoni sun amince za su kafa Kwamitin Sauraren Koke-koken wadanda SARS su ka taba kashe wa ‘yan uwa ko kuma wadanda SARS su ka take wa hakki.
“Kowace jiha za ta gaggauta biyan diyyar wadanda SARS su ka kashe, ko su ka ci wa zarafi ko su ka lahanta.
“Gwamnonin Najeriya na yin tir da harin da aka ki wa Gwamna Adegboyega Oyetola na Osun, wanda wasu batagari dauke da makamai su ka kai masa, a lokacin da ya ke wa masu zanga-zangar #EndSARS jawabi, a Osogbo.
“Mun kuma amince da dukkan bukatun masu zanga-zanga cewa za mu inganta gudanar da kyakkyawar kuma ingantacciyar gwamnati mai nagarta da karsashi.
“A karshe mu na rokon a tsaida zanga-zanga haka nan, domin ci gaba da yi zai kara dagula matsalar tattalin arziki. Sannan kuma batagari ka iya kwace akalar zanga-zangar ta hanyar rika kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Su rika satar kayan jama’a da kuma lalata dukiyoyi.” Inji sanarwar Gwamnonin Najeriya.