Za a tabbatar an yi adalci ga dukkan wadanda ‘yan sanda su ka ci wa zarafi – Ahmed Lawan

0

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce Majalisar Dattawa za ta tabbatar an bi hakkin dukkan wadanda ‘yan sandan Rundunar SARS da aka rushe su ka ci wa zarafi.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, Lawan ya kara da cewa Majalisar Dattawa za ta kara tabbatar da cewa dukkan alkawurran da gwamnati’ ta ce za ta cika wa masu zanga-zanga, ta cika su.

Ya ce alkawurran da su ka hada da gyara fasalin aikin dan sanda ta ingantacciyar gwamnati, duk za a cika su.

“Ina kara tabbatar wa matasa cewa Majalisar Dattawa za ta yi aiki tukuru tare da bangaren zartaswa domin a tabbatar an bi hakkin wadanda SARS su ka ci wa zarafi. Kuma sauran alkawurran da aka daukar masu duk za a aiwatar da su.

“Amma kuma ina kira matasa a guje daukar doka a hannu, domin mun jajirce cewa dukkan wadanda su ka ci zarafin jama’a za a hukunta su.

“Abin takaici ne yadda batagari su ka karbe akalar zanga-zangar #EndSARS, har su ke kai hare-haren lalata dukiya da kwasar kayayyaki.” Inji Lawan.

Lawan ya mika ta’aziyya ga iyalan jami’an tsaron da su ka rasa rayukan su a hannun masu zanga-zanga. Sannan ya ce za a kawo karshen barnar da batagari ke yi.

Ya ja kunnen matasa su guji daukar doka a hannu har su na lalata dukiyar gwamnati da wadda ba ta gwamnati ba.

Share.

game da Author