Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya bayyana cewa za a ninka yawan filayen jiragen sama da ke kasar nan domin saukaka zirga-zirga da kuma bunkasa tattalin arziki.
Sirika ya yi wannan bayani a ranar Talata a lokacin da ya ke gabatar da kasafin 2021 na Ma’aikatar Harkokin Sufurin Jiragen Sama.
Ministar Harkokin Kudade da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Zainab Ahmed ce ta shirya gabatar da kasafin wanda ministoci daya bayan daya za su rika gabatarwa.
Sirika ya ce gwamnati ta fahimci bunkasa yawan filayen jiragen sama a kasar nan, zai marmatso da ci gaban tattalin arziki sosai da kuma saukaka zirga-zirga.
“Kafin karshen 2023 za mu rubanya yawan filayen sauka da tashin jiragen sama, domin muhimmancin su ga inganta tattalin arzikin Najeriya.”
A cikin Kasafin 2021, za a kashe naira bilyan 5 wajen inganta tsaro da samar da kayan kariya da tabbatar da samun lambar ingancin filayen jirage.
Sai kuma naira bilyan 14 da za a kashe wajen gina titin sauka da tashin jirage a filin Jiragen Abuja.
Akwai kuma naira bilyan 1.6 da za a kashe wajen fadada titin saukar jirage a filin jirgin Murtala Mohammed na Lagos.
Za a kashe bilyan 1 a filin jiragen Enugu da wata naira bilyan 1 a filin jiragen Abeokuta.