ZAƁEN ONDO: Gwamna Akeredolu ya yi wa sauran ƴan takara laga-laga a mazaɓarsa

0

Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya samu ƙuri’a 413 a rumfar zaɓen za, yayin da sauran jam:iyyu 16 har da PDP su ka tashi da jimillar kuri’u 33.

Rumfar zaben Akeredolu na a karkashin Mazaba ta 6, Rumfa ta 06 a Ijebu Owo, a garin Owon

Sakamakon da aka fitar ya nuna cewa jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 12 kacal, yayin da ZLP ta Mataimakin Gwamna ba ta samu kuri’a ko daya ba.

Sauran jam’iyyu 7 sun samu kuri’a 1 kowace, yayin da jam’iyya daya ta samu kuri’a 9. Wata kuma ta samu 2. Sai wata daya mai kuri’a 3 kacal.

Tun da safe da wakilin PREMIUM TIMES ya isa garin su Akeredolu, wato Owo, babban birnin Karamar Hukumar Owo, ya tabbatar da cewa kaf a garin duk tutocin APC ne, bai ga tutar PDP ko ZLP ko ta wata jam’iyya daya ba.

Da alama sakamakon zaben na nuni da cewa dukkan ‘yan takara manya su uku na APC, PDP da ZLP, kowa ya lashe mazabar sa da tazarar kuri’u masu yawan gaske.

Kowane dan sandan takara dai ya na Shiyyar Sanata daban da sauran.

Share.

game da Author