Ɗan takarar zaben gwamnan jihar Edo a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Ize-Iyamu, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba za ta je kotu domin su ƙalubalanci sakamakon zaɓen 19 Ga Satumba da aka gudanar a jihar ba.
Iyamu ya yi wannan bayani a ranar Litinin a Abuja.
Sai dai kuma ya ce tabbas za su ci gaba da shari’ar da ke gaban su, wadda su ka shigar tun kafin zabe, inda su ka kalubalanci rashin cancantar dan takarar PDP, Gwamna Godwin Obaseki, wanda ya kayar da shi da kuri’u masu tarin yawa.
Ize-Iyamu ya ce za su ci gaba da waccan shari’a ce da ke kotu, domin ita ma jam’iyyar PDP akwai kararraki daban-daban har 13 da ta maka APC din a kotu, duk a kan zabe.
“Kuma ko a ranar 2 Ga Oktoba sai da aka zauna sauraron wata daga cikin karar da PDP ta kai APC.” Inji shi.
“Da jaridu da kungiyoyi ke cewa an yi sahihin zabe, ba gaskiya ba ne. Ba a yi zabe mai adalci ko sahihi ba. Domin an yi tashe-tashen hankula, a ranar zabe har mutum biyu. An baddala adadin yawan wasu kuri’u. Kuma an firgita masu jefa kuri’a.”
Obaseki ya samu kuri’u 307, 955, shi kuma Iyamu ya samu 223,629.
“Na yanke shawara ba zan ƙalubalanci sakamakon zaɓen ba, saboda biyayya ga manyan jam’iyya, waɗanda su ka yi azarɓaɓin amincewa da sakamakon zaɓen.
“Kuma babban dalili, saboda kawai ba ni son tayar da wata tashin-tashinar rigima ko zaman dar-dar a Jihar Edo.” Inji Ize-Iyamu.