Yeriman Zazzau Mannir Ja’afaru ya taya sabon sarkin Zazzau Ahmed Bamalli murna

0

Sanar da sabon sarkin Zazzau ke da wuya, sai Yeriman Zazzau, kuma wanda shima ya nemi kujerar sarautar Zazzau din ya mika sakon taya murbna ga sabon Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli.

Mannir wanda dan tsohon sarkin Zazzau, Ja’afaru Dan Isyaku ne ya yi wa sabon sarki fatan Alkhairi da rokon Allah ya taya shi riko.

Idan ba a manta ba Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanaran da zabin Magajin Garin Zazzau Ahmed Bamalli sabon sarkin Zazzau ranar Laraba.

Garin Zariya ya barke da murna a lokacin da sabon Sarki ya isa fada bayan sanarwan.

Share.

game da Author