‘YAN BINDIGA A KANO: An yi garkuwa da matar wani basarake

0

Masarautar Karaye a Jihar Kano ta bada sanarwa cewa wasu ‘yan bindiga sun gudu da matar Dagacin Tsara da ke cikin Karamar Hukumar Rogo.

Rahoton ya ce Hakimin Karaye kuma Wamban Karaye, Muhammadu Mahraz ne ya kai rahoton ga Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar.

‘Yan bindigar sun afka cikin gidan Aliyu Muhammad su ka tafi da matar mai suna Aishatu.

Kakakin Masarautar Karaye Haruna Gunduwawa, ya ce an yi awon-gaba da matar wajen karfe 1 na dare.

Ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sai da masu garkuwar su ka rika harbi sama da bindigogin su, kafin su yi gaba da matar dagacin a gaban sa.

Ya ce mazauna garin sun lissafa kwafsar harsasai 17 wadanda masu garkuwar su ka harba a kofar gidan dagacin, kafin su tafi da matar sa.

Gunduwawa ya ce saboda tsoro mazauna garin duk da daji su ka kwana.

Ya kuma ce har zuwa wayewar gari yau Talata ba a san dalilin yin garkuwar da ita ba.

Rogo wacce ta yi iyaka da Jihar Kaduna, an samu rahotannin garkuwa har sau hudu a Karamar Hukumar a cikin wata biyu.

Sarkin Karaye ya yi kiran kara masu jami’an tsaro, shi kuma Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sanda a Kano, Abdullahi Kiyawa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa har yau ba su samu rahoton yin garkuwa da matar ba

Share.

game da Author