Yadda Ta’ammali da miyagun kwayoyi suka yi muni a tsakanin matasan yankin Kudancin Kaduna – Kukan shugaban CAN na Kaduna

0

Shugaban kungiyar Kiristoci CAN na jihar Kaduna, John Hayab, ya nuna bacin ran sa kan yadda shaye-shayen muggan kwayoyi, Barasa, da abubuwa masu bugarwa suka zama ruwan dare a a tsakanin matasan yankin kudancin Kaduna.

Hayab ya bayyana haka ne da yin kira ga matasa da su rika nesanta kan su daga wadannan dabi’u a wajen taron yin addu’oi da yi wa Allah godiya kan zaman lafiya da aka samu a yankin a wadannan yan kwanaki bayan fama da yankin tayi da kashe-kashe a tsakanin mazauna, a garin Kafanchan.

Hayab ya yi kira ga malaman adini, iyaye mata da maza su taimaka wajen ja wa ‘ya’yan su kunne da yi musu horo kan illolin dake tattare da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

” Matasa sun maida shaye-shaye abin burgewa, a koda yaushe kawai suna buge. Su basu zauna lafiya ba haka kuma mutanen dake kewaye da su basu zauna lafiya saboda kwakwalwar a jirkice take.

” Idan ka sha giya ko kayan maye, ko da makiyinka ya kawo maka hari, babu abinda za ka iya yi, saboda a buge kake. Haka kuma idan babu makiyin da zaka afkawa, karshenta ka afka wa naka ne, wato abokai ko ‘yan uwa. Ba zaka yi galaba akan makiyinka ba idan a buge kake.

Bayan haka Hayab ya ce kungiyar CAN zata rika tallafa wa mata a yankin domin su daina yin burkukutu da giyar Bammi da ke ko ina a yankin ana yin shi wanda da zarar mutum yana neman abinda zai sha ya bugu gashinan a kofar gidan sa kawai sai dai ya kwankwana.

Ya ce za a tallafa musu da koya musu sana’oin hannu da basu jari domin su daina yin burkutu da bammi, ko hakan zai rage yawan masu sha, sannan kuma da yin kira ga gwamnati suma su saka hannu a haka domin cigaban matasa da gyara al’umman yankin.

Share.

game da Author